An bayyana wani mutum da milyan N20

An bayyana wani mutum da milyan N20

 Wata budurwa ta nemi shawara ga dandalin sadarwa cewa ta kyale wanda zata aura bayan ce mata da yayi ta maida naira miliyan 20 din da dadiron ta ya bata.

Wata budurwa ta saka labarin tsaka mai wuya da ta shiga a dandalin sadarwa kuma abun ya watsu. Budurwar ta bayyana cewa ta kusa yin aure, kuma ta matukar kaunar wanda zata aura.

An bayyana wani mutum da milyan N20

Sai dai har yanzu tana tare da dadiron nata wanda yake da aure saboda yana da kudi, kuma yana bata kyautuka, wanda zata aura ya hakura da taren su matukar basa wata mu'amula ta saduwa da dadiron.

Dadiron nata ya bata kyauta har na kimanin kudi miliyan N20 a matsayin gudun mawar aure, shi kuma mijin yaki amincewa da kyautar, yanzu dai haka tana neman shawara.

Ga abunda ta tattauna da kawarta.

"Ina tare da wanda zan aura kimanin shekara 1, yana da ilimi, yana aiki a wani banki, da albashin shi dubu N250, yana zaune a unguwar Surulere jahar Lagos, yana tuka mota kirar Honda accord ta shekarar 2009, amma ina da wani dadiro da nake tare da shi kusan shekara 4, yana da kudi, kuma yana da aure, yaman kyautar mota kirar Range a bikin zagayowar haihuwa ta, na fada ma wanda zan aura, yace ba damuwa matukar bama mu'amular saduwa da shi, bayan na yarda da zan aure shi, yace in tashi gidan da dadirona ya kama man a Lekki, in koma gurin shi a Surulere, to yanzu kuma tace in bama mahaifina motar da dadiron ta saya man, saboda baya jin dadin ganin motar, ina matukar son wanda zan aura, amma bazan iya dena rayuwar jin dadi ba.

"Duk abunda yace inyi, nayi, kawai motar nake ji, iyayena sunce in bar motar inji abunda ya ce nan, amma abokai sunce kar na yarda."

Bayan ba fada ma dadirona zanyi aure, yayi man fatar alheri, yace ya san wata rana irin wannan zata zo, ya bamu gudun mawar miliyan N20, amma wanda zan aura yace in maida mai da kudin ko inyi sadaka da su, ban san me zanyi ba, in fasa auren ne kowa ya kama gaban sa ko in bi abunda ya ce"ban san me zanyi ba" amma ina son shi sosai.

Sai kawar tace mata in kin ki auren matsala, in kika cigaba da abunda kike ma matala wannan gaskiya ya wuce sani na, saboda ban san abunda zance maki ba, zan saki a addu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel