Yadda an ceta yan matan Chibok

Yadda an ceta yan matan Chibok

A Nigeria, ana ta ci gaba da murna da kuma bayyana ra’ayoyi game da kubutar 21 daga cikin ‘yanmatan nan na Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace, wadanda suka sami ‘yancin kansu har ma suka sadu da mataimakin shugaban kasar, Yemi Osinbajo jiya a Abuja. 

Yadda an ceta yan matan Chibok

Mataimakin shugaban kasar, wanda yace kubutar yaran abin yabawa ce, ya musanta rahottanin dake cewa “ba ni gishiri, in baka manda” aka yi tsakanin gwamnati da ‘yan Boko Haram, inda aka saki wasu kwamandoji hudu na BH din kafin su kuma su sako ‘yan matan.

Shima ministan watasa labaran Nigeria Lai Mohammed ya dora nasarar samo ‘yanmatan akan abinda ya kira “cijewar da aka yi wajen gudanarda tattaunawa da sulhuntawan da suka haifar da aminci” ne a tsakanin saassan biyu (gwamnati da Boko Haram.)

Rahottani sunce kungiyar bada agaji ta Red Crossda gwamnatin kasarSwitzerlandne suka jagoranci tattaunawar da ta kai aka sako ‘yanmatan, kuma hukumomin na Nigeria sunce za’a ci gaba da tattaunawar don neman kubutar da sauran ‘yanmatan da suka rage a tsare a hannun ‘yan BH.

Tun a watan Afrilun 2014 ne dai mayakan BH suka yi awon gaba da ‘yanmatan su kusan 300 daga wata makarantar sakandare dake garin na Chiboka jihar Borno. Da yawansu sun samu sun gudu, amma dai har yanzu akwai 219 a tsare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel