Yan matan Chibok: Yan Najeriya 5 sun yabi Buhari

Yan matan Chibok: Yan Najeriya 5 sun yabi Buhari

- A jiya, 13 ga watan Oktoba ne yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram suka saki 21 da cikin yan matan Chibok sama da 200 da akayi garkuwa da su a makarantan sakandaren Chibok a jihar Borno

- Shugaba Buhari ya samu labarin sakinsu kafin ya je kasar Jamus domin tattaunawa

- A madadinsa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yayi laale marhabun ga yan matan a fadar shugaban kasa dake Abuja

Ga shahrarrun yan Najeriya 5 da suka yabi shugaba Buhari akan wannan yunkuri.

1. Asiwaju Bola Ahmef Tinubu

Yan matan Chibok: Yan Najeriya 5 sun yabi Buhari
Tinubu

Babban jigon APC na kasa, Bola Ahmed Tunubu yayi matukar nuna farin cikinsa game da ceto yan matan da akayi. Ya bayyana hakan ne a wata jawabin da mai magana da yawunsa Rahman ya saki a jiyan. Asiwaju Tinubu ya mika godiyarsa ga Shugaba Buhari , rundunar sojin Najeriya akan jajircewansu wajen fitittikar yan kungiyan boko haram.

2. Atiku Abubakar

Yan matan Chibok: Yan Najeriya 5 sun yabi Buhari

Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma jigon jam'iyyar APC, Alh Atiku Abubakar ya yi farin cikin ceto rayuwar yan matan chibok 21. Duk da cewan akwai sauran da ke hannun boko haram har yanzu, tsohon shugaban kasa ya yabi shugaba buhari akan wannan nasara.

3. Gwamna Kashim Shettima

Yan matan Chibok: Yan Najeriya 5 sun yabi Buhari

Gwamnan jihar Barno, Gwamna Kashim Shettima ya fi kowa farin cikin sakin yan matan Chibok. Zaku tuna cewa gwamna yayi bayani a taron shugabannin arewan da akayi a jihar kaduna inda ya yabi shugaba Buhari kuma ya siffanta shi a matsayin mai ceton su a yankin arewa maso gabas. Gwamna Kashim bai tsaya a nan ba ya nuna farin cikinsa ga sakin yan matan da akayi.

4. Oby Ezekwesili

Yan matan Chibok: Yan Najeriya 5 sun yabi Buhari

Tsohuwar mataimakin shugaban bankin duniya kuma Shugaban kungiyar Bring Back our girls,watau a kungiyar fafitikan ganin cewa an ceto yan matan Chibok, Oby Ezekwesili, tayi wata jawabi mai dadi ga gamsarwa na nuna farin cikinta da kuma mika godiyan ta ga Shugaba Muhammadu Buhari akan yunkurin ganin cewa an ceto yan matan Chibok. Oby Ezekwesili wacce ta lashin takobin cewa bazasu daina zanga-zanga har sai idan an ceto yan matan, yanzu an share mata hawayenta

5. Mikel Obi

Yan matan Chibok: Yan Najeriya 5 sun yabi Buhari
Mikel Obi

Shahrarren dan kwallon kafan nan, Mikel Obi, bai yadda aka bar sa a bay aba wajen mika tutar yabo ga shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa akan nasarar sakin yan matan Chibok guda 21

Asali: Legit.ng

Online view pixel