Ana binciken mai a jihohin Arewa

Ana binciken mai a jihohin Arewa

- Hukumar NNPC na binciken mai a Arewacin kasar, sun tura kayan aiki jihar Gombe da Bauchi

- Kamar yadda shugaban kasa Buhari ya bada umarnin ci gaba da binciken mai, kamfanin ta haka rijiyoyi 23 a tasar Chad (Chad basin)

Ana binciken mai a jihohin Arewa

A matsayin wani bangare na binciken mai a Arewa, hukumar Nigeria National Petroleum Corporation (NNPC) sun yi shirin tura kayan aiki kuma su fara neman mai a jihar Bauchi da Gombe, cewar shafin ma’aikatar kamfanin.

Maikanti Baru, daraktan hukumar NNPC, ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyara jihar Bauchi.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Boko Haram sun saki wasu yan matan Chibok

Yace: “Mun zo nan ne don nuna sigina ga Mutanen Bauchi da Gombe masu karamci kan nufinmu da kokarin shigar da kayayyakin aikinmu zuwa tasar Gongola (Gongola basin)

 “Hakika ayyukanmu a tasar Chadi zai dawo sabo da zaran mun samu bayyanannan aya a guri” Baru ya bayyan.

Sannan shugaban na NNPC ya shawarci mutanen jihohin da kada su tayar da fitina lokacin da suka ga ana shigar da kayayyakin neman mai a cikin garuruwansu.

Baru ya kara da cewa wan aka binciko a johohi biyu a baya suna da sahihanci sosai, masamman a daya daga cikin rijiyoyin Yankari.

A baya hukumar Legit.ng ta bayyana cewa hukumar NNPC ta tabbatar da cewan zuwa yanzu an kamfanonin mai sun rigada sun haka rijiyoyin mai guda 23 wanda suka hada da binciken mai a Arewa tun shekaru 30 da suka wuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel