Matan Chibok: Tinubu yace har hankalin sa ya fara kwanciya

Matan Chibok: Tinubu yace har hankalin sa ya fara kwanciya

- Wani Jigo a Jam’iyyar APC mai mulki ya yabawa Shugaba Buhari game da kubuto wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok

- Bola Tinubu Ya kuma jinjinawa Sojojin Kasar da suke ta kokarin fada da ‘gan Boko Haram

- A jiya ne aka saki wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok da aka sace fiye shekaru biyu da suka wuce

Matan Chibok: Tinubu yace har hankalin sa ya fara kwanciya

Wani Jigo a Jam’iyyar APC mai mulkin Kasar nan ya yabawa kokarin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari game da kubuto wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok da ‘Yan Kungiyar Boko Haram suka sace fiye shekaru biyu da suka wuce. Bola Tinubu Ya kuma yabawa Kokarin Shugaban Kasar da kuma Sojojin Najeriya wajen kubuta ‘Yan matan Chibok din.

Bola Tinubu ya ce hankalin Shugaba Buhari ba zai kwanta ba har sai an kubutar da ragowar ‘Yan matan da aka sace. Bola Tinubu ya yi murna game da ‘Yan matan Chibok din da suka kubuta daga Boko Haram. Ya kuma ce kowa zai kawo gudumuwar sa wajen samun lafiyarv wadannan yara da kuma dawowar su daidai.

KU KARANTA: Sojoji sun nemi Yan Boko Haram su sallama

Tunde Rahman, wani mai magana da bakin shi Bola Tinubu ya bayyana cewa wannan labara na dawawar ‘Yan matan Chibok har guda 21 abin murna ne da farin ciki. Bola Tinubu yace har ya kuma fara samun sa’ida. Bola Tinubu ya kuma taya ‘Yan uwan matan Chibok din murnar dawowar ‘Ya ‘yan su.

A dai jiya ne wasu mata har guda 21 daga cikin wadanda ‘Yan ta’addan Kungiyar Boko Haram suka sace tun Afrilun 2014 suka dawo gida.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel