Willian ya rasa mahaifiyarsa

Willian ya rasa mahaifiyarsa

- Dan wasan Chelsea na tsakiya Willian ya rasa mahaifiyar shi jiya

- Willian ya jefa kwallo a wasar da kasar Brazil suka lallasa kasar Venezuela

- Kungiyar Chelsea sun aika sakon ta'aziyya

Dan wasan tsakiya na kungiyar Chelsea ya rasa mahaifiyar sa jiya, bayan fama  da tai tayi da ciwon kansa na tsawon shekara 2, Willian din dai ta dawo London in da ya rubuta a shafin sa na twitter cewa mamar shi ta warke a farkon kakar wasar bana.

Willian ya rasa mahaifiyarsa
Willian

Willian din ya jefa kwallo a wasar da kasar shi ta Brazil ta doke kasar Venezuela da ci 2-1, mahaifiyar shi dai ta mutu jiya kuma za'a jana'izar ta a garin su dake San paolo ranar alhamis 13 ga watan satumba.

Kungiyar Chelsea ta aika sakon ta'aziyya ga Willian inda suka ce" kungiyar Chelsea da magoya bayan ta suna cikin juyayi, mun tausaya maka matuka, muna jin abunda kake ji.

In zaku iya tunawa a wasar da Chelsea ta lallasa Hull city willian ta zura kwallo in yace ya sadaukar da kwallon da ya zura ga mamar shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel