Gwamnatin Bauchi ta kubutar da 'yan mata 450 da aka sace

Gwamnatin Bauchi ta kubutar da 'yan mata 450 da aka sace

- Gwamnatin jihar Bauchi ta taimaka wajen kubutar da 'yan mata 450 da aka sace

- An bayyana kubutowar a ranar kula da yara mata kanana ta kasa da kasa watau 11 ga Oktoba 2016

- An sada yaran mata da iyayensu

Gwamnatin Bauchi ta kubutar da 'yan mata 450 da aka sace
makamai

Hakika rana ce ta farin ciki a jihar Bauchi yayin da hadin kai tsakanin gwamnatin jihar Bauchi da jami'an tsaro ya jaza kubutar da 'yan mata 450 daga masu safarar  mutane.

Bayanan dake fitowa lokacin da ake bikin ranar yara mata kanana ta kasa da kasa wanda ya kama 11 ga Oktoba 2016, wata mamba ta wata kungiya mai son ganin ci gaban mata ta jihar Bauchi koko High Level Women Advocates (HILWA) ta bayyana kubutowar.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bani fili- Orubebe ya daukaka kara

HILWA wanda kungiya ce mai zaman kanta ta shirya bada bayanin tare da hadin gwuiwar hukumar bayar da ilmi na matakin farko ta jihar Bauchi (SUBEB ) da kuma hukumar kananan Yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF).

Kalimatu Abdulkadir, jami'a ce a ma'aikatar ilmi tace ma'aikatar ta sami bayani cewa an kawo yara mata kanana daga Zamfara, Jigawa da Sokoto, an kuma kaisu Abuja bayan an raba su gida biyu. Jami'an tsaro sun gano su a Abuja suka kuma kubutar dasu, sa'annan suka sada su da iyayensu, cewar jaridar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel