Gwammanatin tarayya ta bani fili- Orubebe ya daukaka kara

Gwammanatin tarayya ta bani fili- Orubebe ya daukaka kara

- Godsay Orubebe ya daukaka hukuncin da CCT ta yanke mai                                    

- A cikin kotun daukaka kara ta Abuja, yace gwamnatin tarayya ta bashi fili      

- Tsohon ministan harkokin NejaDelta yace ya riga ya siyar da filin

Bayan hukuncin da kotun CCT ta yanke, tsohon ministan harkokin NejaDelta Godsay Orubebe ya daukaka kara a kotun daga kara ta Abuja. Orubebe ya roki kotun daukaka kara ta Abuja, ta janye hukuncin da kotun CCT ta yanke mai ranar 4 ga watan Oktoba 2016.

Gwammanatin tarayya ta bani fili- Orubebe ya daukaka kara
Godsday Orubebe a kotu.

Karar da akayi a kotun CCT wadda mai shari'a Danladi Umar ya shugaban ta, ta samu Orubebe da yin karyar bayyana kadarorun shi a shekara ta 2007, daya daga cikin laifukan shi be bayyana yana da fili mai lamba 2057 a Asokoro Abuja.

CCT ta bada umurnin cewa mallakar gurin ya zama laifi., sai dai ya daukaka kara ta hannun lauyan shi mista Selikeowei Larry SAN. Yayin da yake daukaka Karar, ya kawo wasu dalilai 3 wadanda za su sa kotun daukaka kara tayi watsi da hukuncin CCT.

Da farko dai yace wanda kwamitin mutane 2sunyi kuskuren kai matsaya gurin yanke hukun cin da be samu shaidu ba.

Kamar yadda Orubebe yace wanda an yanke mai hukunci ba tare da wani shaidu ba wanda ze iya kawo saba ma doka.

Yace ban samu filin mai lamba 2057 ta hanyar cin hanci ba ko saye ba filine mara komai a daji wanda gwamnatin tarayya ta bani kyauta a matsayin hakkokin duk wanda ta taba rike makamin minista.

Ya kara da cewa yana da kwararan shaidun cewa ya sayar da filin ga wani kamfani mai suna Divention properties Limited, kuma manajan kamfanin Akinwumi Ajobola ya tabbatar da haka a kotun CCT.

Lokacin da CCT ta ke yanke hukuncin, Orubebe yace" na yanke hukuncin ba wanda nake haya a gidansa, lauya Ajibola dan biyan kudin haya na shekara 2.

Mai shari'a, a kasar nan mutane da yawa basu san albashin minista ba, tun daga abunda ya fara daga gurin zaman shi, tafiye-tafiyen shi, da komai duk wata a shekara ta 2007 a na bashi miliyan 1.3, a shekara ta 2008 a n rage kudin zuwa 990,000.

Dan haka albashin minista, a da, da yanzu ba ze iya biyan haya ba a unguwannin da suka dace kamar Asokoro, mai tama, da sauran su.

Kowanne minista ana yi mai kyauta, da naga wannan kyautar sai nayi amfani da damar na biya haya, mai shari'a ban taba ganin filin ba ko takaddun shi, ranar da aka ban, ranar na sayar a kudi miliyan 10, miliyan 5 kenan kowace shekara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel