Yan Real Madrid zasu ji dadin wannan abun da ya same su

Yan Real Madrid zasu ji dadin wannan abun da ya same su

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Jamus, Toni Kroos, ya sabunta yarjejeniyarsa da Real Madrid domin ci gaba da buga mata tamaula zuwa 2022.

Dan kwallon mai shekara 26, wanda ya koma Bernabeu daga Bayern Munich a shekara 2014, ya ci wa Madrid kwallaye hudu a wasanni 108 da ya buga mata.

A watan Satumba aka yi ta rade-radin cewar dan kwallon zai koma Manchester United da taka-leda, domin maye gurbin Paul Scholes.

Mujallun Spniya sun wallafa cewar Kross zai dunga karbar fam 346,000 a kowanne mako a kungiyar ta Real Madrid.

A wani labarin kuma Tsohon shugaban hukumar alkalan wasa ta Ingila, Keith Hackett, ya yi korafi kan nada Anthony Taylor a matsayin wanda zai yi alkalancin wasan da za a yi tsakanin Manchester United da Liverpool.

A ranar Litinin Liverpool za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan Premier da za su kara a Anfield.

Hackett ya ce gidan da Taylor ke zama yana mil shida tsakaninsa da filin Old Trafford, wanda hakan zai iya kawo zargin magudi a karawar.

Ya kuma kara da cewar babu wanda zai ce Taylor ba shi da kwarewa, amma duk wani zargi da zai taso idan aka samu matsala, yana da tushe.

Taylor bai taba hada sabga da United ba, hasalima kungiyar Altrincham yake marawa baya, wadda take buga National League a Kudancin kasar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel