Ya shiga hannu yayin da yake kokarin satan yara

Ya shiga hannu yayin da yake kokarin satan yara

A jiya Laraba 12 ga watan Oktoba an kama wani matashi da ake zarginsa da sana’ar yin garkuwa da mutane yayin da yake kokarin satan wasu yara yan makaranta su biyu a jihar Benue.

Ya shiga hannu yayin da yake kokarin satan yara

Dududu wanda zargin bai wuce shakaru 20 da yan kai ba, yan banga ne suka kama shi a garin Otukpo na jihar Benue da misalin karfe 8 na safe. Sai dai yayi karfin hali inda ya tsere daga hannun yan banga, amma jama’an gari sun mai tara tara sukayi ram! da shi.

Ana zargin barawon ne da yunkurin satan wasu kananan yara yan makaranta su biyu, amma Kaakakin rundunar yansandan jihar Moses Yanu yace basu samu wani rahoto kan batun ba.

Ga hotunan lamarin

Ya shiga hannu yayin da yake kokarin satan yara
Matashin a hannun yan banga

KU KARANTA: Jimillar kudaden da EFCC ta kwato a watanni 10

Ya shiga hannu yayin da yake kokarin satan yara
Matashin a hannun yan banga

A wani labarin kuma, majalisar wakilan kasar nan ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari daya sanya dokar tabaci game da satan mutane a kasar nan. jaridar Daily Report tace majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya data kira taron masu ruwa da tsaki wanda ya kunshi dukkanin hukumomin tsaron kasar, da dukkanin kamfanonin sadarwa da kwamitocin da abin ya shafa daga majalisun dokokin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel