Kungiyar lauyoyin Najeriya sun tabbata kan matsayin su

Kungiyar lauyoyin Najeriya sun tabbata kan matsayin su

A dai dai lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriya ke bada tabbaci da kuma karfin gwiwa ga bangaren shari’a na Najeriya, cewa binciken da ake yiwa bangaren Shari’a ba anayi bane don rage karfin Shari’a ko tozarta Alkalai bane illa yaki da cin hanci da rashawa.

Kungiyar lauyoyin Najeriya sun tabbata kan matsayin su
BAYELSA State Chief Judge, Justice Kate Abiri

Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya NBA na ci gaba da kwatantawa mahukuntan kasa da kuma jama’a, cewa hanyoyin da aka bi wajen aiwatar da binciken shine ake ganin ba dai dai bane a cikin demokaradiyya, kuma wata kila anyi ne da gayya domin a domin a tozarta wasu bisa dalilai na siyasa.

A wata hira da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk yayi da ‘daya daga cikin mambobin kungiyar NBA Barista Abdulhamid Mohammed, ya nuna cewa kungiyar ba wai tana yaki da hana binciken cin hanci da rashawa a bangaren Shiri’a bane, amma dai wajibi ne abi dokokin Najeriya da ka’ida wajen aiwatar da binciken ba tare da anci mutunci ko tozarta bangaren Shiri’a ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel