Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa kasar Jamus

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa kasar Jamus

Shugaban kasa Najeriya Muhammadu Buhari ya bar kasar zuwa kasar Jamus ziyarar kwanaki biyu daga 13 zuwa 15 ga watan Oktoba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa kasar Jamus
President Buhari and Chancellor Merkel

Mai bawa shugaba Buhari shawara kan kafofin yada labarai, Femi Adesina ya ce shugaban zai gana da Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Markel kan batutuwan da suka shafi sha’anin tsaro, tallafawa ‘yan gudun hijira a arewa maso gabashin kasar da kuma alakar tattalin arziki.

Ana saran Shugaba Buhari zai kuma gana da mazauna Najeriya a kasar bayan ya halarci taron bunkasa kasuwanci da zai gudana a babban birnin kasar Berlin, wanda mafi yawanci kamfanonin Jamus da ke Najeriya zasu halarta.

A wani labarin kuma da dumi-dumin sa wani babban jami'in gwamnatin Najeriya ya shaida wa BBC cewa an saki 'yan matan Chibok 21 daga cikin 217 da ke hannun kungiyar Boko Haram.

Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Sehu ya tabbatar da labarin, inda ya ce 'yan matan na hannun jami'an tsaro a Maidiguri da ke jihar Borno.

A cewarsa, an ceto matan ne sakamakon tattaunawar da gwamnati ta yi da shugabannin kungiyar ta Boko Haram.

Ya ce a nan gaba kadan ne za a bayyana sunayen matan da aka saka. Garba Shehu ya kara da cewa suna sa ran ceto mutum 3000 da 'yan Boko Haram ke ci gaba da tsarewa.

A baya an sha fitar da labarai marasa tushe kan sakin 'yan matan na Chibok.

Sakin matan Chibok 21 wata babbar nasara ce ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, wacce take shan suka daga wajen masu fafutikar ganin an ceto 'yan matan.

Kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan fiye da 250 daga makarantar sakandare ta Chibok a watan Afrilun 2014 - lamarin da ya ja hankalin duniya sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel