An saki yan matan Chibok 21

An saki yan matan Chibok 21

Jami’in gwamnatin Najeriya ya bayyana wa hukumar BBC cewan an saki mutane 21 daga cikin yan matan Chibok da yan kungiyar Boko Haram suka sace.

An saki yan matan Chibok 21

Yan matan Chibok

Wani babban jami'in gwamnatin Najeriya ya shaida wa BBC cewa an saki 'yan matan Chibok 21 daga cikin 217 da ke hannun kungiyar Boko Haram.

Jami'in ya nemi kada a bayyana sunansa, kuma har yanzu gwamnati ba ta fitar da sanarwa kan lamarin ba.

A baya an sha fitar da labarai marasa tushe kan sakin 'yan matan na Chibok.

Kawo yanzu babu wani cikakken bayani kan yadda aka kubutar da 'yan matan.

KU KARANTA KUMA: Musulman Kungiyar Shi'a sunyi taron Ashura

Sai dai BBC ta fahimci cewa suna can a hannun jami'an tsaro a birnin Maiduguri, na jihar Borno.

Kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan fiye da 250 daga makarantar sakandare ta Chibok a watan Afrilun 2014 - lamarin da ya ja hankalin duniya sosai.

Wasu daga cikin iyayan yaran da aka sace sunyi kira a kan shugaban kasa Buhari lokuta da dama kan cewa ya nemo masu yaransu. Inda har suka bukaci da ya saki mayakan nasu kamar yadda kungiyar ta bukata domin a sake masu yaransu.

Munji cewa iyayen yaran karkashin kungiyar BingBackOurGirls sunyi zanga-zanga a fadar shugaban kasa kwanakin baya domin suna ganin gwamnati batayi komai a kan ceto yaran ba.

Ku kalli wani bidiyo na wasu daga cikin iyayen Yan matan Chibok.

Source: Legit

Mailfire view pixel