Labari da dumi: Boko Haram ta sako yan matan Chibok 21

Labari da dumi: Boko Haram ta sako yan matan Chibok 21

Kungiyar yan ta’adda ta Boko Haram ta sako yan matan Chibok su 21, a cewar rahoton jaridar Sahara Reporters.

Labari da dumi: Boko Haram ta sako yan matan Chibok 21

Sahara Reporters ta ruwaito cewa da safiyar ranar alhamis 13 ga watan Oktoba ne kungiyar Boko Haram ta sako yan matan.

Idan ba’a manta ba, a shekarar 2014 ne kungiyar Boko Haram ta sace daliban makarantar mata na garin Chibok, inda zuwa yanzu an samu labarin wasu daga cikinsu sun mutu, wasu sun tsere, yayin da sauran suke kame hannun yan kungiyar Boko Haram.

KU KARANTA: An gano daya daga cikin Yan matan Chibok

Wata majiya daga bangaren gwamnati ta bayyana mana cewar Boko Haram ta ajiye matan ne a garin Banki na jihar Borno, daga nan kuma jami’an rundunar soji ta kwashe su a cikin jirgi mai tashin angulu.

Sako yan matan da Boko Haram tayi a jiya ya faru ne, watanni kadan bayan kungiyar ta bukaci gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari data sakar mata wasu daga cikin mayakanta muddin suna son ta sako yan matan Chibok.

Labari da dumi: Boko Haram ta sako yan matan Chibok 21

Sai dai zuwa yanzu ba’a sani ba ko su waye daga cikin yan matan aka sako ba, kamar yadda ba’a san wasu mayakan kungiyar Boko Haram gwamnati ta saka ba.

Ku kalli wannan bidiyo:

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel