Gwamnatin Tarayya ta kori Ma’aikatan FAAN

Gwamnatin Tarayya ta kori Ma’aikatan FAAN

- Gwamnatin tarayya tana daidata sahun ma’aikatar jiragen sama na kasar

- Yanzu haka gwamnatin tarayya ta kori wasu manyan ma’aikata daga hukumar kula da filin jiragen sama na Kasar

- An kori manyan darektoci da manajoji na Hukumar kula da filin jiragen sama na kasar watau FAAN

Gwamnatin Tarayya ta kori Ma’aikatan FAAN

 

 

 

 

A wani shiri da Gwamnatin Tarayya ta ke yi na daidata sahun Ma’aikatar Jiragen sama na Kasar ta zazzage wasu manyan ma’aikatan Hukumar kula da filin jiragen sama na Kasar watau FAAN. Tun dai farkon hawan wannan Gwamnati ake shirin aiwatar da wannan mataki.

Wannan mataki dai ya kawo sauyin lamari a Ma’aikatar Jiragen sama na Kasar. Gwamnatin Tarayya ta dai kori manyan Darektoci na ma’aikatar, sannan kuma da Manajoji da ma Mataimakan su. Hakan dai wani shirin garambawul ne da Gwamnatin Tarayya ke kokarin yi.

KU KARANTA: Wani yace wa Tinubu Allah ya kara

Wata majiya daga Daily Trust ta bayyana cewa yanzu ma aka fara korar, domin kuwa ana sa ran cewa wasu za su biyo baya nan gaba. Sai dai duk da cewa Gwamnatin Tarayya ba ta fitar da jawabi game da lamarin ba, Ministan Sufuri na Kasa, Rotimi Amaechi ya sa hannu game da koran.

Ma’aikatan dai da aka kora, dama tun can ba su cika sharudan aiki ba, an dai umarce su da su mika shugabanci ga ma’ikatan da suka fi dadewa a Ma’aikatar. A baya dama dai Shugaban ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Misis Winfried Oyo ta bada shawarar a rage yawan ma’aikatan da ke wurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel