Abubuwa 6 da Buhari zai yi maganin Boko Haram

Abubuwa 6 da Buhari zai yi maganin Boko Haram

- Najeriya na fama da rikicin Boko Haram da ya ki ci, ya ki cinyewa duk da nasaraorin da sojoji ke ikirarin samu kan ‘yan kungiyar

- Wasu kwararru a kan yaki da ta’addanci sun bayyana wasu abubuwa 6 da ya kamata gwamnatin Buhari ta yi idan ta na son ganin bayan kungiyar

Abubuwa 6 da Buhari zai yi maganin Boko Haram
Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram

Ofis mai kula da ayyukan ta’addanci da kuma yaki da tsattsauran ra’ayi, ya fitar da wani rahoton sakamako na kasar kan ta’addanci a shekarar 2015, Cibiyar hada hannu don yaki da ta’addanci na kasashen da ke Sahara, mai samun tallafin gwamnatin Amurka, an kafa shi ne don karfafar hadin gwiwa tare, da karfafar ayyukan soji, da tabbatar da doka, tare da hadin kan fararen hula a arewaci da kuma yammacin Africa, don yakar ayyukan ta’addanci.

Idan har Najeriya na so ta rabu da fitinar ta’addancin Boko Haram, cibiyar ta ce sai kasar ta aiwatar da wadannan abubuwan:

1. Karfafawa da kuma habaka ayyukan soji

Karfafawa da kuma habaka ayyukan sojojin kasashen da ke arewaci da kuma yammacin Africa, gami da tabbatar da bin doka, da oda, don samun nasarar yaki da ta’addanci.

2. Hadaka

Hadaka dangane da kwazon sojojin arewaci, da kuma yammacin Africa, don tabbatar da bin doka da oda, gami da taimakawa abokan hulda, don a samu hadin gwiwa na yaki da ta’addancin, don a gudu tare, a kuma tsira tare.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram ta yi ajalin masu sarauta 100 -Shehun Borno

3. Inganta tsaron iyaka

Inganta tsaron kan iyaka don sa ido, da hanawa, da kuma dakile duk wani kai-komo, na yaki da ta’addanci,

4. Tabbatar da bin doka da oda

Inganta doka, da oda, da kuma saukaka gudanar da hukuncin sharia, da kuma bincike, da hukunta ayyukan ta’addanci a kan kari.

5. Sa Ido

Sa ido kan ayyukan ta’addanci, da dakile hanyoyin daukar nauyinsa (Kamar satar mutane da ire-irensa)

6. Dakile hanyoyin samun goyon baya

Rage yadda jama’a ke iya tausayawa, da kuma ba da goyon bayan ayyukan ta’addanci

An kafa cibiyar a shekara 2015 da kasashen Algeria, da Burkina Faso, da Cameroon, da Chad, da Mali, da Mauritania, da Morocco, da Niger, da Nigeria, da Senegal, da kuma  Tunisia a matsayin mambobi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel