Far ma Alkalai somintabi ne, akwai saura - Majiya

Far ma Alkalai somintabi ne, akwai saura - Majiya

- Wata majiya a fadar shugaban kasa tace akwai sauran Alkalai da za'a tuhuma

- Wannan na faruwa ne bayan an far ma Alkalai a karshen makon da ya gabata

- An baiwa EFCC umurni da lasisin damke duk masu Almundahana

Far ma Alkalai somintabi ne, akwai saura - Majiya

Da alamun cewa damke Alkalai da Hukumar DSS tayi a karshen makon da ya gabata somintabi ne yayinda wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana ce za'a fadada binciken.

An damke wasu Alkalau a daren ranan juma'a ,8 ga watan oktoba inda aka damke su ,Amma game da Vanguard, za'a sake damke wasu.

Wata majiya a fadar shugaban kasa tace ana shirin tsaftace bangaren shari'a kuma bashi bukatan baiwa EFCC ko DSS umrni kafin suyi aikinsu.

KU KARANTA: Labari da dumi: Boko Haram ta sako yan matan Chibok 21

Majiyar tace shugaban kasa ya samu rahoton majalisan shari'a akan damke alkalai da akayi.

Shugaban kasa yayi alkawarin cewa ba zai sa baki a binciken ba amma yace za'a fadada bincike

 “Bashi bukatan bada umurnin komai. EFCC da DSS na da yancin kansu. Zasu oya aikinsu. Amma zan iya fada muku cewa shugaba ba zai sa baki ba. Irin shugaban kasan da muke da shi.

“Babu gudu ba ja da baya. Wannan bincike mai fadi zamuyi. Hakane, shugaban kasa ya karbi rahoton NJC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel