Matasan jihar Kano sun kai hari ga yan Shi'a

Matasan jihar Kano sun kai hari ga yan Shi'a

- Matasan jihar Kano sun kai hari ga kungiyar yan Shi’a a kano a lokacin da suke zagayensu

- Dole yan kungiyar suka tsere don tsira a lokacin da matasan suka kai masu hari da wukake

- Dole kuma yan sanda suka kare yara kanana da mataye soboda yanayinsu

Mambobin kungiyar musulman Najeriya wanda aka fi sani da Shi’a sun fuskanci matsala a jihar Kano yayinda matasa suka kai masu hari da makamai.

Matasan jihar Kano sun kai hari ga yan Shi'a

Kungiyar wanda aka saw a doka a jihar Kaduna sun samu hari daga matasa da sukayi fushi sun kuma ji masu raunuka da makamai.

KU KARANTA KUMA: Oba Akiolu ya zargi Obasanjo da horar da jihar Lagas

An kai harin a kan yan kungiyar a ranar Laraba, 12 ga watan Oktoba lokacin da aka kai hari makamancin wannan a kan yan kungiyar dake jihar Kaduna inda mambobi 13 suka rasa rayukansu yayinda da dama suka ji rauni.

Matasan jihar Kano sun kai hari ga yan Shi'a

A cewar Sahara reporters, yan shi’an sunyi zagaye a Kano lokacin da wasu matasa suka far masu da hari cikin fushi da wukake, adduna da takobi.

Zagayen nay an kungiyar Shi’a yazo ne lokacin da jihar ta hana ko wani irin zagayen addini amma matasan suka yi kokarin karya doka

Matasan jihar Kano sun kai hari ga yan Shi'a

An rahoto cewa mambobin kungiyar sun tsere don tsira bayan an kai masu harin. yawancinsu sunyi gaggawan cire bakaken kayan da suka sanya saboda matasan suna saurin farma duk wanda suke sanye da bakaken kaya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel