Yarinya musulma a Nasarawa wadda taga kuros, ce zata warkar

Yarinya musulma a Nasarawa wadda taga kuros, ce zata warkar

Ganin kuros kusa da babban masallacin Assakion a garin Lafiya ya kawo rudani, yayin da iyayen ta suka boye wadda ta ga kuros din.

Hajara Husseini, yarinya musulma wadda ta ce taga kuros din kusa da babban masallacin a jahar Nasarawa, tana shirye da warkarwa da yin wasu abubuwan al'ajabi.

Yarinya musulma a Nasarawa wadda taga kuros, ce zata warkar

Sai dai, da iyayen ta suka ji haka, sai suka boye yarinyar suka kaita jahar Bauchi.

Yarinyar taga kuros din kusa da masallaci misalin  karfe 7: 35 na yamma, 28 ga watan satumba tare da wasu yaran mata guda 2, iyayen sun dauke ta bayan sunyi addu'a tare da wasu mutane fararen fata guda 2 da suka ziyarci gurin.

Mamakin ganin kuros din kusa da masallaci ya janyo hankalin dandazon jama'a. Sai dai tun lokacin ba'a kara ganin Hajara ba.

Yarinya musulma a Nasarawa wadda taga kuros, ce zata warkar

An ruwaito cewa iyayen ta sun kaita Bauchi, inda ainahin mahaifin ta yake zuwa aiki kafin ya musulunta, amma an ruwaito cewa bata cin komai, hasali ma tana rokon iyayen ta da su maida ta Assaikio ta gama abunda Ubangiji ya umarce ta da tayi a gaban kuros din.

Ganin kuros din kusa da masallaci ya saka mutane na kusa da na nesa yin gamgamin zuwa dan yin addu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel