An gargadi Buhari kan jonathan

An gargadi Buhari kan jonathan

- A wasu bayanai da ya yi, John Paden marubuci littafin tarihin rayuwar shugaba Muhammadu Buhari, ya ce shugaban yana da hujjojin da zai iya kama Jonathan da laifin cin hanci da rashawa ya kuma daure shi

- Wannan bayani na marubucin yayi ya harzuka wasu ‘yan Najeriya har aka shiga luguden lebe a shafukan sada zumunta da muhawara na Intanet, wasu ma na gargadin Buhari da kar ya kuskura ya taba Jonathan

An gargadi Buhari kan jonathan

A littafinsa mai suna ‘Muhammadu Buhari: kalubalen shugabanci a Najeriya,’ John Paden Sheihun Malami a nazarin al’amuran kasa da kasa, ya rubuta cewa, abin da ke gaban Shugaba Buhari shi ne kwato dukiyar al’umma da aka sace ba daure mutane ba, a kuma ce, Buhari ya na da wasikun da ke nuna cewa, Jonathan ya bukaci amfani da wasu kudaden ba sa cikin kasafin kudi.

Sai dai wannan ikirari na Farfesa Paden yayi, ya  janyo ka-ce-na-ce a dandalin sada zumunta da muhawara daga wasu ‘yan Najeriya, wadanda ke zargin shugaba Buhari da bita-da-kulli ga wanda ya gada, a mamakon nemo yadda zai fitar da kasar daga karayar tattalin arziki.

Wasu kuma na gargadin cewa, duk wani yunkurin aikawa da Jonathan gidan yari ba zai haifarwa da wannan gwamnati da mai ido ba, wasu kuma sun fito kakara suna yin barazana ne ga shugaban da ya taba Jonathan ya ga abinda zai faru da kasar, a ra’ayin wasu kuma, shi ma Jonathan na da wasu hujjojin da zai iya daure Buhari a lokacin yana mulki, wasu kuma na shakkun hujjar da shugaban yake da ita kan Jonathan.

Har yanzu hukumar na ci gaba da binciken matar tsohon shugaban kasar Dame Patience Jonathan, kan miliyoyin dalolin, da kuma inda ta samo su, baya ga shari’oi daban-daban da EFFC ke yi da na hannun daman Jonathan kan batar wasu miliyoyin nairori na sayen makamai, da kuma kudaden yakin neman sake zabensa a shekara 2015.

A baya a lokacin yana mulki ya taba ikirarin cewa, sata ba cin hanci ba ne ko rashawa, ko don haka ne wasu goyonsa duk da abin da aka aikata na satar dukiyar al’umma? Menene ra’yin ku kan wannan batu? Sai ku garzaya shafinmu na Facebook ku fadi albarkacin bakinku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel