Masu zanga-zanga sun afka ma sakatariyar APC

Masu zanga-zanga sun afka ma sakatariyar APC

- Masu zanga-zanga sun mamaye sakatariyar APC suna neman a cika alkawurran da akai masu kafin zaben 28 ga September na Edo

- Wasu mambobin sunyi barazanar tona asiri in ba'a biya masu bukatunsu ba

- APC na zargin PDP da hannu cikin zanga-Zangar matasan

Masu zanga-zanga sun afka ma sakatariyar APC

An mamaye sakatariyar All Progressive Congress (APC) wadda ke kan titin airport a cikin birnin Benin jiya 12 ga Oktoba daga wasu masu zanga-zanga wadanda aka ce sunyi aikin wucin gadi da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a zaben gwamnan jihar.

KU KARANTA:An kama barayi a majalisar dokokin tarayya

Masu zanga-zangar wadanda mafi yawansu matasa ne, a cewar Vanguard sun taru a gaban ofisoshin APC wajen Karfe 11 na safe, suka kuma nace sai sun ga wani jami'in jam'iyyar kafin su bar wurin. Matasan sun ce sun zartar da shawarar nuna bakin cikin su domin kin cika alkawarin da aka yi masu cewa za'a saka masu bayan zaben 28 ga Satumba. Bayan sunyi jiran kusan awowi biyu, wasunsu sunyi barazanar tonon silili idan ba'a biya masu bukatunsu ba.

Amma yayin da yake maida martani, sakataren watsa labarai na APC a jihar mista Godwin Erhahon, ya nisanta jam'iyyar da duk wasu alkawurran da aka yi ma ma'aikatan wucin gadin.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel