Kasar China ta nada Jakada zuwa duniyar Mars

Kasar China ta nada Jakada zuwa duniyar Mars

- Kasar China ta nada wani tsohon dan wasan kwallon kwando a matsayin jakadar ta Duniyar Mars

- Kasar ta China ta tura Yao-Ming a matsayin jakadar ta zuwa duniyar

- An nada wasu mutane goma kuma dama a matsayin Jakadu zuwa duniyar

Kasar China ta nada Jakada zuwa duniyar Mars

 

 

 

 

 

 

Kasar China ta nada wani Tsohon dan wasan kwallon kwando a matsayin Jakadar duniyar Mars mai suna Yao Ming. Yao-Min ya bugawa Kungiyar kwallon Kwandon Houston Rockets lokacin da yake buga wasa.

Ban da kuma dan wasa Yao Ming, Kasar China ta zabi wasu mutane goma kuma dabam a matsayin Jakadun Kasar zuwa duniyar ta Mars. Kasar China na kokarin aika jirgin satalai na sama jannati zuwa duniyar ta Mars nan da shekarar 2020.

KU KARANTA: Ga mutumin da ya fi kowa shan dauri a duniya

Nan da shekarar 2020 kasar China na shirin aikawa da jirgi zuwa duniyar ta Mars wanda ke kusa da duniyar nan ta mu.

Wannan jirgi dai zai rika amfani da karfin rana ne wajen aiki. Bayan tsohon dan wasan kwallon kwandon, kasar China ta zabi wasu mutanen kuma a matsayin jakadun na ta, sun hada da; wani marubuci mai suna Liu Xing, da wata matashiyar ‘Yar wasar Kwallo mai suna Lang Ping.

Duniyar Mars ce mai makwabtaka da mu, sai dai dabam ta ke da ta Dan Adam, duk akwai alamun rayuwa da fitowar tsirrai, duniyar na da matukar kura. Kasar China na ta kokarin kafa tarihi a wannan fage na ilmin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel