Duncan Mighty yayi suka kan aure

Duncan Mighty yayi suka kan aure

- Sanannen mawaki a Najeriya Duncan Mighty ya saka hoton auren wata karamar yarinya da akayi a Zamfara

- Ya soki lamarin inda ya roki mutane da su fito su goyi bayan sa, dan kawar da auren kananan yara

Duncan Mighty Okechukwu, sanannen mawaki ne a Najeriya, an san shi da wata waka da yayi mai taken Port Harcourt boy, an haifeshi kuma ya tashi a garin Obio-Akpor jahar Rivers.

Duncan Mighty yayi suka kan aure

Dan gane da abun da ya saka ba dadewa a shafin sa na Instagram, mawakin yayi magana kan aurar da kananan yara.

Ya saka hoton wata amarya karamar yarinya da bata yin farin ciki da auren da akai mata, kuma ya bayyana tsananin kin lamarin.

Duncan Mighty yayi suka kan aure

Yace wanda dan Allah mutane na ku ara man muryoyin ku dan ganin karshen aurar da kananan yara, yawan cin kananan yara da basu isa aure ba suna samun ciwon yoyon fitsari gurin haihuwa, wanda ze iya halaka su, nakasar da su.

Kananan yara karatu suke bukata ba namiji ba, wannan abun ya faru a jahar Zamfara. Kuma ya nemi da a taya shi tallar hana yaduwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel