EFCC ta sako wani dan siyasar Abia Uche Ogah

EFCC ta sako wani dan siyasar Abia Uche Ogah

- 'Yan awowi bayan tsaron da hukumar hana almundahana tayi masa, Uche Ogah ya samu 'yancin kansa

- Lauyansa, Monday Ubani ya tabbatar da sakin nasa, ya kuma yi bayani kan abin da ya faru da kuma dalilan da yasa aka gayyato shi

EFCC ta sako wani dan siyasar Abia Uche Ogah

Hukumar hana almundahana (EFCC) ta sako mista Uche Ogah, shugaban kampanin man Masters Energy Oil and Gas Limited, awowi bayan kiransa da hukumar tayi zuwa kotun majistaret na Tinubu. Lauyansa Monday Ubani ya fadi haka a wani jawabi daya raba wanda Legit.ng ta samo ranar Litinin 10 ga Oktoba, 2016.

KU KARANTA: DSS ta saki Alkalan Kotun Koli

Hukumar EFCC ta gayyato Ogah, wanda kwanan nan yayi takarar neman kujerar gwamnan jihar Abia tare da Okezie Ikpeazu bayan 'yan sanda sun janye zargin aikata jabu wanda tace an yi shi ba tare da shaidu ba. Ubani yace an sako wanda yake karewa ba tare da wasu sharudda ba, 'yan awowi bayan ya rubuta jawabinsa ga hukumar. Lauyan yace, hukumar ta dauki matakin da ta dauka dalilin zargin da mai kara yayi wanda ya kira "gayyata mai kunyatarwa"

Asali: Legit.ng

Online view pixel