Naira tayi daraja a kasuwannin bayan fagge

Naira tayi daraja a kasuwannin bayan fagge

Darajan Naira ya karu da naira uku (N3) a ranar talata 11 ga watan Oktoba a kasuwannin bayan fagge, inji wani dan canji a jihar Legas.

Naira tayi daraja a kasuwannin bayan fagge

Naira tayi daraja a yau, duba da yadda ake siyar da ita ba akan N473 ga $1 a ranar litinin 10 g watan Oktoba. Amma ana samun dala kan N304.75 a bankuna, ba kamar yadda take N306.71 a ranar litinin ba.

Dan canjin yace hakan ya faru ne sakamakon lasisin da aka baiwa Travelex na gudanar da kasuwancin canjin dala a Najeriya. Ya kara da cewa maido da tsarin baiwa yan canji masu lasisi dala dake gudana a yanzu haka ya sanya naira yin daraja.

KU KARANTA: Yadda wani Uba ya ceci rayuwar yaronsa yayin ambaliya

Shugana yan canji na kasa Aminu Gwadabe yace ya kamata mahukunta su sake duba farashin da ake siyar da dala ga yan canji, don karfafa ma yan Najeriya dake kasashen waje masu siyar ma yan canji dala gwiwa. Yace idan naira ta cigaba da yin daraja, hakan zai magance yadda wasu ke siyan dala daga haramtattun yan canji.

Zaku iya duba farashin dala a shafin mu na Legit.ng, don samun farashi mai sauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel