majalisar wakillai ta gayyaci shugaban hukumar sss

majalisar wakillai ta gayyaci shugaban hukumar sss

Majalisar wakilai ta kira Shugaban Hukumar SSS Lawal Daura da ya zo gabanta domin yi mata bayani kan kama Alkalai da Jami'an Tsaro na Sirri SSS suke yi.

Wani dan majalisa mai suna Mojeed Alabi ya ce bai ga dalilin da zai sa majalisar ta sa bakin ta akan abinda bai shafe ta ba, amma majalisar ta yi watsi da wannan kiran ta ce sai Lawal Daura ya zo gabanta.

A gefe daya kuma majalisar dattijai ta yi watsi da batun gayyato shugaban SSS din kan batun kama Alkalan.

A jiya ne dai Hukumar ‘Yan sanda DSS ta saki dukkanin Alkalan da ta cafke a wani samamen da jami’anta suka kaddamar na yaki da rashawa akan manyan Alkalan.  Rahotanni sun ce hukumar ‘Yan sandan na farin kayan ta bayar da belin Alkalan ne wadanda za ta ci gaba da bincike akansu.

A jiya Talatar ma dai Majalisar Alkalan Najeriya ke gudanar da taro na musamman sakamakon dirar mikiyar aka kai wa wasu manyan Alkalan kasar a daren Juma’a inda ‘Yan sandan farin kaya suka ce sun kwato Miliyoyan daloli a farmakin da suka kai gidajen Alkalan.

Kaddamar da farmaki akan Alkalan dai ya janyo cece-kuce a Najeriya inda kungiyar Lauyoyi da Jam’iyyar adawa ta PDP suka yi allawadai da matakin wanda tare da sukar gwamnatin Buhari.

Alkalan da aka cafke sun hada da na Kotun Koli guda biyu da na Babbar Kotu a Abuja da wasu Jihohin Najeriya.

Babbar Alkalin Alkalan Najeriya Mahmud Muhammad ya yi allawadai da samamen wanda zai jagoranci taron Majalisar Alkalai a yau Talata a Abuja.

Majalisar Alkalan dai ta ki ba hukumar SSS hadin kai domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da Alkalan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel