Shi'a: Jihohi arewa 5 da ka iya haramta tarukan addini

Shi'a: Jihohi arewa 5 da ka iya haramta tarukan addini

- Haramta mazhabin Shi’a jihar Kaduna da gwamnati ta yi, babu mamaki hakan ya sa cikin sauran kungiyoyin addini ya duri ruwa na ko za su iya samun damar tarukan addini

- Gangamin da ‘yan Shi’a suke yi, a ko’ina a cikin manyan da kuma kananan garuruwan Najeriya ya zama abin kwatance a bisa dalilai da yawa, zai wuya sauran jihohi sun lamince hakan

Shi'a: Jihohi arewa 5 da ka iya haramta tarukan addini
Shugaban yan shia, Ibrahim Zakzaky

Dangane da al’amarin da faru ga mazhabin Shi’a a Kaduna ya sa muka waiwayi wasu jihohi 5 na arewacin Najeriya da ake ganin ba za su laminci tarukan gangami masu nasaba da addini ba, izina da irin gangamin ‘yan shi’a da kuma irin matakin da jihar Kaduna ta dauka da kuma la’akari da yanayin jihohin musamman ta fuskar yanayin zaman lafiya da dangataka tsakanin addinan kasar.

1. Kano

Ita ce ta farkon da daukar mataki a matsayin riga kafi, domin a ranar Litinin 10 ga watan Oktoba ne kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya ba da sanarwar ta kafofin yada labaran jihar na haramta duk wani gangami na taron jama’a da ke da nasaba da addini.

Wannan ba abin mamaki bane, la’akari da yawan jama’a mabanbantan addini, da kusaci da Zaria cibiyar ‘yan Shi’ada da kuma watakila irin abin da ka iya biyo baya bayan haramcin da aka yiwa kungiyar a Kaduna.

2. Katsina

Taron mauludin Sheikh Ibrahim Niass na ‘yan tarikar Tijjaniyya, da aka yi a babban birnin jihar, ya tara dubban mutane a ‘yan watannin da suka wuce, an kuma yi lafiya an tashi lafiya, sai dai zai yi wuya gwamnatin jihar ta sake lamince irin wannan gangagamin taro na addinin a jihar a yanzu.

Jihar na da mabiya mazhabin Shi’a da yawa, ganin cewa da akwai daya daga cikin na hannun daman shugaba Zakzaky, Yakubu Musa da aka hallaka a rikicin ‘yan kungiyar da sojoji a Zaria, dangane da haramcin kungiyar a Kaduna da kuma hana su taruka Kano, zai yi wuya gwamnatin Katsina ta kyale tarukan addini musamman zanga-zanga daga kowacce kungiyar addini.

3. Borno

Jihar da ta ke farfadowa daga hare-haren kungiyar Boko Haram, ta na kuma fama da rikicin ‘yan gudun hijira, zai yi wuya a ko a mafarki lamince wani taron gangami na addini ballantana wata zanga-zanga.

4. Nassarawa

Ganin kusancin su da babban birnn tarayya Abuja, babu mamaki ga masu son gudanar da tarukan addini su nemi yi a unguwanni  irin su Karu, da Marrraba da kuma sauran unguwanni masu makwabtaka da fadar gwamnatin tarayya, sai dai bisa hasashe, zai yi wuya gwamnatin jihar ta amince, ganin yadda ‘yan shi’a suka sha barkonon tsohuwa a cikin Abuja a wata arangama da suka yi da ‘yan sanda a lokacin suke tarwatsa su.

5. Filato

Jihar da ake kokarin wanzar da zaman lafiya sakamakon rikice-rikicen addini da kabilanci, a bisa hasashe, zai yi wuya gwamnatin jihar ta lamince wani gangamin taro, ko kuma zanga-zanga mai nasaba da addini, musamman na mazhabar Shi’a.

Baya ga haka kungiyoyin Izala 1 da ta 2 masu da’awar bin tarfarkin sunnah zalla, nan ce shalkwatarsu, kuma sun yi hannun riga da akidar Shi’a, kuma sun dade da kiran gwamnati ta haramta kungiyar, ta kuma dauki mataki kan shugabanta Ibrahim Zakzaky.

Asali: Legit.ng

Online view pixel