Sarkin musulmi yayi magana rikicin manoma da makiyaya

Sarkin musulmi yayi magana rikicin manoma da makiyaya

- Sarkin daular Usmaniyya yayi magana akan hayaniyan makiyaya da manoma

- Sarkin musulman ya nisantar da kanshi daga makiyaya kuma yace a ladabtar da su

Sarkin musulmi yayi magana rikicin manoma da makiyaya

Sarkin musulmi ,Muhammad Sa’ad Abubakar III,yayi kira ga ukubantar da fulani makiyaya a ranan 10 ga watan oktoba.

Sarkin wanda dan asalin Fulani ne ya nisantar da kanshi daga makasan, ya ce kada a kuskure fulani muslumai da makiyaya saboda zaman lafiyan Najeriya.

Sultan din wanda yayi magana a taron kwana biyu na jihohin arewa akam tsaro ,tattalin arziki,da siyasa a jihar Kaduna.

KU KARANTA:An rufe kamfanin dake dinka kayan aikin yansanda na bogi a Legas

“Mutanen na da hadari masu kisa. Amma suna aikin kansu, yan iska kuma a dauke su yan iska. Saboda haka gwamnatin tarayya su ladabtar da su.

“Abun bakin ciki ne ace idan mutane suka ji ance Fulani na son musuluntar da Najeriya kuma dalilin da yasa suke kisa kenan. Duk bafullacen da yayi kisa ba kabilar fulani yake mawa ba kuma ba addinin musulunci ba.

Yayinda yake cigaba da Magana ,yace arewan yau ba irin arewan da Sardauna ya bari bane, Sardauna yayi kokarin hada kan kabilun arewa amma yanzu abin ya saba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel