Libya ta koro yan Najeriya 154

Libya ta koro yan Najeriya 154

Wani rahoto daga jaridar The Nation ya tabbatar da cewa an koro yan Najeriya da yawansu ya kai 154 daga kasar Libya a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba.

Libya ta koro yan Najeriya 154

Majiyar tace hukumar shige da fice ta duniya c eta taimaka wajen dawo da mutanen Najeriya bayan rikicin kasar Libya ya rutsa dasu. Daga cikin wadanda aka koro har da masu kokarin tsallakawa nahiyar turai.

Hukumar shige da fice ta kasa tace da misalin karfe hudu na yamma ne jirgin kasar Libya kirar A330-200 mai lamba 5A-LAT dake dauke da mutanen ya sauka a filin tashin jirgi na tunawa da Murtala Muhammed.

Jami’an tsaro daga mayakan rundunar sojan sama, da na hukumar shige da fice, hukumar yansanda, IOM da hukumar bada agajin gaggawa ne suka tarbe yan Najeriya da aka koro daga kasar Libya.

Daga cikin su akwai mata 96, maza 58, kanana yara 3, mata masu juna biyu 9 sai wasu marasa lafiya su 3. Sa’annan sun samu rakiyar likitan hukumar shige da fice ta duniya (IOM) Abusrewi Zakariya don kulawa da marasa lafiyan cikinsu.

KU KARANTA: Yan kungiyar asiri sun hallaka shugabansu

Shugaban IOM a jihar Legas Nahashon Maina Tuo yace wannan shi ne karo na hudu cikin wannan shekara da suke taimaka yan Najeriya da suka nuna bukatar dawowa gida daga Libya.

Sai dai kasa da watannin 6 kenan da aka hankado wasu yan Najeriya su 172 daga kasar ta Libya, wanda daga cikin su akwai karamin yaro dan shekara 12 da mata guda biyar, su dai mutanen suna kan hanyarsu ta zuwa nahiyar turai ne daga Libya yayinda gwamnatin Libya ta kama su. daga nan aka yi hadin gwiwa tsakanin gwamnatin, da ofishin jakadancin Najeriya dake Libya da IOM wajen dawo dasu gida Najeriya.

Ga wasu daga cikin hotunan su.

Libya ta koro yan Najeriya 154
Libya ta koro yan Najeriya 154
Libya ta koro yan Najeriya 154

Asali: Legit.ng

Online view pixel