Gwamna Dickson yace yana bin tsohon gwamna Sylva bashi

Gwamna Dickson yace yana bin tsohon gwamna Sylva bashi

- Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson yace yana bin tsohon gwamnan jihar Timipre Sylva bashin wasu kudi

- Dickson yace tun shekarar 2012 har yau bai bada wannan kudi ba

- Kotu ce dai ta umarni tsohon gwamna Sylva da ya biya Gwamna Dickson wannan kudi bayan shari’ar su

Gwamna Dickson yace yana bin tsohon gwamna Sylva bashi

 

 

 

 

 

 

Gwamnan Jihar Bayelsa, Seriake Dickson ya bayyana cewa yana bin wani tsohon Gwamna na jihar watau Timipre Sylva bashin wasu kudi har Naira dubu dari biyar. Gwamna Dickson yace tun shekarar 2012 Kotu ta bada umarnin Sylva da ya biya sa wadannan kudi.

Kotu ta umarni Tsohon Gwamna na Jihar ta Bayelsa Timipre Sylva ne da ya biya mai girma Seriake Dickson wadannan kudi a madadin ci masa zarafi da yayi. Kotun Koli ta Kasar ta nemi Sylva da ya biya Gwamna Dickson wannan kudi har rabin miliyan bayan ya bata masa lokaci a Kotu.

KU KARANTA: Shugaba Buhari yace da alama fa sai ya sa karfin Soja

Mista Daniel Iworiso-Markson, Sakataren yada labarai na Jihar Bayelsa ya bayyana hakan a jiya. Iworiso-Markson yace har yanzu kuwa shi wannan Tsohon Gwamna Sylva bai biya wadannan kudi da ake bin sa ba.

Jami’in yada labaran dai yana magane game da karar da Sylva ya kai Kotu, Timipre Sylva wanda Tsohon Gwamna ne na Jihar Bayelsa, yayi takara wannan karo ma da Mista Dickson, wanda ya kara buga sa da Kasa. Mista Daniel Iworiso-Markson yace da Sylva ya san darajar Kotu da ya biya kudin da ta ce ta biya tun shekaru hudu da suka wuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel