EFCC ta binciki tsofaffin Gwamnonin CBN - Femi Falana

EFCC ta binciki tsofaffin Gwamnonin CBN - Femi Falana

 - Babban Lauyan nan mai kare hakkin jama’a Femi Falana yayi kira ga Hukumar EFCC da ta binciki tsofaffin Gwamnonin Babban bankin Kasar nan

- Femi Falana yace ya kamata EFCC ta binciki yadda Bankuna suka rika karbar bashi daga babban bankin Kasar

- An bada wannan bashi ne daga shekarar 2006 zuwa ta 2011

EFCC ta binciki tsofaffin Gwamnonin CBN - Femi Falana
Femi Falana

 

 

 

 

Babban Lauyan nan mai kare hakkin jama’a Femi Falana SAN yayi kira ga Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya da ta binciki tsofaffin Gwamnonin Babban bankin Kasar watau CBN saboda wasu bashi da aka rika ba Bankunan Kasar nan a wani lokaci.

Femi Falana ya rubuta takarda ga Hukumar EFCC game da batun, sai dai yace har yanzu shiru. Babban Lauyan Kasar Femi Falana yace akwai bukatar a sani ko cewa Bankunan sun biya bashin da aka ba su zuwa asusun Najeriya.

KU KARANTA: Babban Lauya Femi Falana yace anyi daidai ga Alkalai

Femi Falana SAN yace ba zai yiwu muna kukan rashin kudi ba kuma bayan muna bin bashi a baya. Lauya Femi Falana yace dole a binciki lamarin, sannan a karbo kudin, kana a hukunta wanda duk aka kama da laifi.

Babban Lauyan, Femi Falana yace wani Tsohon Gwamnan Babban bankin Kasar watau CBN ya bada bashin kudi har dala biliyan bakwai ($7b) ga wasu bankuna guda 14 a shekarar 2006. A shekarar 2011 kuma wani Gwamnan bankin ya kara ba wasu bankuna aron dala biliyan biyar ($5b).

Asali: Legit.ng

Online view pixel