An kama wasu mutane da kawunan mutane a cikin burodi

An kama wasu mutane da kawunan mutane a cikin burodi

An kama wasu mutane guda biyu dauke da kawunan mutane a cikin burodi a jahar Legas a cewar jaridar Nation.

Mutane dai sune, Jamiu Alabi dan shekara 24 da kuma Yemi John da shekara 32 sun shiga hannun hukuma a ranar Asabar da daddare wanda yazo daidai da 8 ga watan Oktoba, a matsayar bus dake church a Ipaja.

An kama wasu mutane da kawunan mutane a cikin burodi

An kuma ce an kama mutanen ne da kawunan mutane guda uku a cikin burodi. Inda akowane burodin suka rubuta sunayen mutane kamar haka, Danjuma N20,000, Yusuf N70,000, Alhaji Mumuni N10,000.

Mai magana da yawun yan sandan yankin Dolapo Badmos yace, sunakan bincike akan al'amarin.

Haka kuma ya tabbatar da kama wasu yan fashi a titin Shibiri akan titin Imude a Ojo, bayan da suka kwacema wata mata mai suna Ifeoluwa Francis kayan ta.

Wanda suka hada da wani mai suna Sugun Ariyo dan shekara 17 da kuma Michael Adetona dan shekara 16.

Inda suka kwace mata N20,000 da wayar hannu kirar Blackberry Z3 da kuma katin waya. Haka kuma an kamasu ne alokacin da suke kokarin raba abinda suka sata a wajen ta.

Allah ya kyauta!

Asali: Legit.ng

Online view pixel