Ana zargin 'yan sanda da karkatar da kudaden tsaro

Ana zargin 'yan sanda da karkatar da kudaden tsaro

- Jami'an 'yan sanda 240 sun koka kan rashin biyansu alawus na aikin tsaron zaman lafiya na shekarun 2013 zuwa 2015

- Suna zargin bacewar kudaden kan almundahana tsakanin hukumar 'yan sanda da ma'aikatan ECOWAS

- Hukumar 'yan sanda tace bata da masaniya game da batan kudaden amma IG yace suna sane ba'a biya alawus din ba

Ana zargin 'yan sanda da karkatar da kudaden tsaro
jami'an yan sanda

Kusan jami'an 'yan sanda 240 sun koka kan zargin karkatar da kudaden alawus nasu na aikin tsaron zaman lafiya da wasu ma'aikatan gwamnatin tarayya tare dana kungiyar tattalin arziki na kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) suka yi. Vanguard ta ruwaito cewa kudaden na aikin da akayi a Guinea Bissau ne tsakanin shekarun 2013 da 2015, amma ba'a biya jami'an ba.

KU KARANTA: Sabuwa: EFCC ta damke mai rejistan Babban Kotun tarayya

Adalci da tallafin kawo zaman lafiya a ECOWAS zasu nakasa yayin da ake kokarin kawo kwanciyar hankali da damokradiyya a Afrika ta yamma idan ECOWAS tare da hadin kan gwamnatin Najeriya zasu karkatar da kudaden daya kamata a biya jami'an da suka yi aikin zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel