Alkalan Kotun koli 6 da suka tsallake kamun DSS

Alkalan Kotun koli 6 da suka tsallake kamun DSS

Mutanen Najeriya sun waye gari a ranan Asabar, 8 ga wtan oktoba da labarin cewa jami’an DSS sun kai farmaki gidajen Alkalan kotun koli.

Alkalan Kotun koli 6 da suka tsallake kamun DSS
T

A wata usulubi, ta fasa gidajen su inda ta samu kudade masu dimbin yawa na fitan hankali. Ana sa ran za’a gurfanar da wasu a cikinsu a yau litin,10 ga watan oktoba.

Duk da hakan akwai Alkalan Kotun kolin da abun bai shafa ba. Jaridar Legit.ng ta tattaro muku wadannan Alkalai

Sha Karatu:

Jastis Mary Odili

An nada ta Alkaliya a kotun koli ne a shekarar 2011. Ta kasance matar gwamnan jihar Ribas daga shekaran 1999-2007. Ba sunanta cikin wadanda aka far ma.

Alkalan Kotun koli 6 da suka tsallake kamun DSS

Jastis Walter Onnonoghen

Shine mafi babban Alkali a kotun kolin kuma shine zai zama Babban lauyan Najeriya. Duk da cewan wasu kafafan labarai sun sanya sunansa cikin wadanda aka aka damke, bas hi a cikinsu.

Jastis Bode-Rhode Vivour

An nada shi Alkali a Kotun koli a shekarar 2010. Kwanan nan akayi garkuwa da uwargidan sa. Babu sunashi cikin masu kashi a gindi.

Jastis Muntaka Connmassie

Ya shiga Kotun Koli a shekarar 2008. Kafin nan, ya kasance Alakalin kotun daukaka kara a Fatakwal, Flato, Abuja ,Ilori, da Benin. Babu sunansa a ciki masu babakere.

Jastis Kudirat Olatokunbo

Alkalan Kotun koli 6 da suka tsallake kamun DSS

An fi sanin ta a Jastis Kekere Ekun, ta shiga kotun koli ne a shekara da ya gabata. Babu sunanta a ciki.

Jastis Kumai Bayang Akaahs

Ya shiga Kotun Koli ne a Shekar 2012 daga Kaduna. Ya kasance mamban kungiyar lauyoyin Najeriya da kuma na duniya. Babu sunan sa a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel