Asirin baragurbi alkalai ya tonu

Asirin baragurbi alkalai ya tonu

- Wasu majiyoyi daga hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun bayyana cewa, ta tsarin daukar hoton yatsun hannu na asusun ajiyar banki ne, jami’an hukumar suka kama alkalai masu cin hanci da rashawa

- Hukumar DSS da ta duba asusun ajiyar alkalan da yanzu aka tsare da su, ta gano cewa sun dade suna karbar cin hanci a yayin gudanar ayyukansu tare da amfani da sunaye da hotunan ‘ya ‘yansu da matansu a asusun ajiyar banki daban-daban

Asirin baragurbi alkalai ya tonu

Wasu majiyoyi na Hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun bayyana cewa, ta tsarin daukar hoton zanen yatsun hannu na asusun banki ne, aka gano miliyoyin nairorin da wasu alkalai suka karba a matsayin hanci.

A yanzu, Hukumar ta damke alkalai bakwai watau, Alkali Inyang Okoro, da kuma Sylvester Ngwuta na Kotun koli, sai Alkali Adeniyi Ademola na babbar kotun ya tarayya da ke Abuja, da Kabir Auta na babban kotun jihar Kano, da Mu’azu Pindiga na babbar Kotun jihar Gombe, da Mohammed Tsamiya na kotun daukaka kara na Ilorin, da kuma Alkalin alkalai na jihar Enugu, IA Umezulike wadanda suke tsare a ofishin hukumar.

KU KARANTA KUMA: Femi Falana yayi kaca-kaca da rubabbun Alkalai

A rahoton da jaridar Vanguard ta wallafa, Hukumar DSS ta duba asusun ajiyyar bankin alkalan da suke tsare a inda ta gano cewa lallai sun dade suna karbar na goro daga hannun mutane daban-daban, a yayin gudanar da ayyukansu na alkalanci, amma suke amfani da sunaye, da kuma hotunan ‘ya ‘yansu da matansu a irin wadannan asusun ajiyar bankin na cuta.

A cewar majiyar: “A yayin da muka tuhumi mata da kuma ‘yan uwan alkalan dangane da takardun da muka samu daga bankuna, sun fada mana cewa, ba su san an yi amfani sunayensu ba a asusun ajiyar.”

Wani abin takaici a cewar rahoton shi ne, yadda daya daga cikin alkalan ya yi basaja, kuma je siyayya a wani kantin zamani, ashe ya je ne ya karbi cin hancin da Dalar Amurka daga daya daga cikin mutanen da yake yiwa sharia, wanda wata kyamarar tsaro ta dauki hotonsu a cikin sirri, ba su sani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel