Hukumar DSS ta gano makudan daloli a wajen manyan Alkalai

Hukumar DSS ta gano makudan daloli a wajen manyan Alkalai

Jami’an Hukumar DSS ta gano makudan kudi har da na kasashen wajen a gidajen manyan Alkalan Kasar

Jami’an farar hula dai sun burma gidaje wasu daga cikin manyan Alkalai na kasar

Gwamna Ayo Fayose na jihar Ekiti ya bayyana cewa Damukaradiyyar Najeriya na fuskantar barazana

Hukumar DSS ta gano makudan daloli a wajen manyan Alkalai

Jami’an farar hula na Kasar da ake kira DSS sun burma gidan manyan Alkalan Kasar na Kotun Koli da kuma wasu manyan Kotu na Kasar. Wasu da dama suna ganin wannan ya lai katsalandan cikin ayyukan bangaren shari’a na Kasar.

Hukumar DSS dai ta bayyana dalilin ta, tace ba ta saba wata dokar Kasa ba, kuma tana girmama Alkalai da Bangaren Shari’a na Kasar. Jami'an Hukumar DSS dai ta samu kudi Naira kusan Miliyan dari, da daloli har na fiye da dubu dari biyar da sauran kudi na Kasar waje a gidajen Alkalan.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai saki Dasuki?

A cikin gidajen da aka shiga dai har da na Alkali Walter Onnoghen wanda ke Kotun Koli, ana dai sa ran shine ma zai zama Shugaban Alkalan Kasar kwanan nan. Hukumar DSS din dai ta bayyana cewa ta gano wasu dala miliyan $2 da Alkalan suka boye a gida. Haka kuma an samu fiye da Naira Biliyan daya da rabi a wajen Alkalan Kotun Koli.

An samu fiye da Miliyan 50 daga gidan Alkali Adeniyi Ademola, da kuma kusan dala $17779 da kuma kudi na Pounds Sterling har 80. Da kudi na Euros da Rupees. Haka kuma an samu fiye $319000 daga hannun Alkali Nawali Ngwuta da Naira fiye da miliyan talatin. A gidan Alkali John Inyang an samu kudi har da na takardun Kasar Ghana da Argentina, da kuma dinbin daloli.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel