Nigerian news All categories All tags
Gwamna Fayose yace Najeriya na cikin matsala

Gwamna Fayose yace Najeriya na cikin matsala

- Gwamna Ayo Fayose na jihar Ekiti ya bayyana cewa Damukaradiyyar Najeriya na fuskantar barazana

- Fayose ya fadi haka ne bayan Jami’an farar hula sun burma gidan manyan Alkalan Kasar

- Gwamnan ya kira ‘yan kasar da kuma Kasashen duniya da su yi wani abu kafin a ga bayan damukaradiyya a Najeriya

Gwamna Fayose yace Najeriya na cikin matsala

 

 

 

Gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose ya bayyana cewa lallai damukaradiyyar Najeriya na fuskantar babbar barazana bayan Jami’an farar hula na Kasar da ake kira DSS sun burma gidan manyan Alkalan Kasar na Kotun Koli da kuma wasu manyan Kotu na kasar.

Gwamna Fayose ya bayyanawa manema labarai a garin Ado-Ekiti cewa yanzu kowa ya gane inda Najeriya ta dosa.

Fayose yace Damukaradiyya na fuskantar babbar barazana daga Gwamnati mai-mulki. Gwamnan na Jihar Ekiti ya kira ga ‘yan kasar Najeriya da kuma Kasashen duniya da su yi wani abu kafin a ga bayan damukaradiyya a Najeriya

KU KARANTA: Ai ni ne canjin Inji Fayose

Ayo Fayose yace sam bai dace Gwamnati ta sa Hukuma ta shiga gidajen Alkalan Kasar nan ba, yace babu wani dalili ko uzurin yin hakan. Fayose yace ana nema ne a tsoratar da Alkalan Kasar. Gwamna Fayose yace Kotu dai ne gidan karshe na adalci a Kasar nan.

Tuni dai Hukumar ta DSS ta bayyana dalilin ta, tace ba ta saba wata dokar Kasa ba, kuma tana girmama Alkalai da Bangaren Shari’a na Kasar. DSS dai ta samu kudi Naira kusan Miliyan dari, da daloli har na fiye da dubu dari biyar da sauran kudi na Kasar waje a gidajen Alkalan.

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel