Sojoji sun kashe yan mata yan kunar bakin wake guda 3

Sojoji sun kashe yan mata yan kunar bakin wake guda 3

- An kashe yan mata yan kunar bakin wake yan ta'addan Boko Haram guda 3 a garin Gwoza                                                 

- Soja 1 ya samu rauni saboda karfin bom din, amma yana amsar kulawa

Sojoji sun kashe yan mata 3 yan kunar bakin wake yan ta'addan boko haram a Gwoza, jahar Borno ranar Alhamis 6 ga watan Oktoba, kafin yan ta'addar su samu damar yin aika-aikar.

An samu labarin faruwar lamarin daga bakin mukaddashin kakakin sojoji Col. Sani Usaman Kukasheka.

Sojoji sun kashe yan mata yan kunar bakin wake guda 3

Kamar yadda ya fada a jawabin shi, matan sunyi yunkurin shiga inda sojoji suke, amma sai yan kungiyar banga suka tona su, wadanda suke tunanin hijab din da suke saye da shi, da yadda sukayi shigar suna dauke da wani abu.

Yadda Col. Usman ya fada wanda yau Alhamis, 6 ga watan Oktoba kusan 12:25 na rana, yan mata 3 yan kunar bakin wake sunyi yunkurin shiga gurin sojoji a Gwoza, jahar Borno.

Yan kunar bakin waken sun shigo ta Pulka, yan banga sun gansu daga nesa, sai suka fada ma sojoji abunda suke zargi, yan banga sun lura da cewa matan sunyi kama da maras gaskiya, suna tafiya da manyan hijabai kuma sun banbanta da mata manoma dake gurin.

Yayin da yan kunar bakin waken suka lura ana ganin su, sai suka yi sauri dan su zo su tada bom din gurin sojoji, sai sojoji suka an kara suka harbe yan kunar bakin wake 2, dayar kuma sai ta ruga cikin daji amma sai sojojin suka bita, abun rashin jindadi shine sojan mu ya samu rauni amma dai yana samun kulawa a asibitin mu, kuma yana cikin koshin lafiya.

Mutuwar yan kunar bakin waken a Gwoza tazo ne bayan sojoji yan Zaman Lafiya Dole suka kashe wani dan kunar bakin wake a wajen garin Maiduguri jahar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel