Kemi Olunloyo ta gargadi Linda Ikeji da E-money

Kemi Olunloyo ta gargadi Linda Ikeji da E-money

Mahawartacciyar yar jaridannan kuma diyar tsohon gwamna wato Kemi Olunloyo, tayi kira ga sanannan ma'abocin jaridar yanar gizo wato Linda Ikeji da dan kasuwannan Emeka Okonkwo (E-money) su tsananta ma kansu tsaro kuma su daina bayyana dukiyarsu a kafafen sadarwa na yanar gizo

Bayan gawurtaccen fashin da aka kaima sanannen tauraron ba'amurkennan wato Kim kardashian, a inda ta ruwaito cewar tayi asarar $miliyan 11 na bama yan fashi, mahawartacciyar yar jaridar wato Kemi Olunloyo wacce bata taba jinkiri wajen bayyana ra'ayinta ta gargadi mutane da su guji bayyana dukiyarsu a kafafen sadrwa na yanar gizo.

Kemi Olunloyo ta gargadi Linda Ikeji da E-money

Kemi Olunloyo tace wata kila Linda Ikeji da E-money su kasance hari na gaba daga yan fashi. A wata tattaunawarta ta kafr sadarwa na tweeter, Kemi Olunloyo tayi gargadi na musamman ga sanannan ma'abocin jaridar yanar gizo wato Linda Ikeji da dan kasuwannan kuma yayan mawaki Kcee wato Emeka (E-money) da su daina bayyana dukiyarsu saboda kar da su jawo hankalin barayi gare su. Kamar yadda ta saba Kemi a shafinta na tweeter ta bayyana dalilan da yasa tayi tunanin sune hari na gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel