Hisbah Ta Kano Ta Dawo da Kwamandan da Aka Dakatar Kan Zargin Karkatar da Tallafin Korona

Hisbah Ta Kano Ta Dawo da Kwamandan da Aka Dakatar Kan Zargin Karkatar da Tallafin Korona

- Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta dawo da kwamandanta na ƙaramar hukumar Dala Suyudi Hassan

- Da farko an dakatar da Suyudi Hassan ne kan zarginsa da karkatar da tallafin COVID-19

- Sai da kwamitin da aka kafa ta yi bincike kan zargin ta ce bata same shi da aikata laifin ba

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta rubuta wasika na dawo da Kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Dala, Suyudi Muhammad Hassan da aka dakatar kan zargin karkatar da tallafin Korona na ƙaramar hukuma, rahoton Daily Trust.

Wasikar mai lamba KN/HB/OPS/88/04/V.II/191 mai dauke da sa hannun mataimakin sakataren hukumar, Muhammad Babangida D/Iya da aka rabawa manema labarai ta ce binciken da aka yi ya nuna bai aikata laifin ba.

Hisbah Ta Kano Ta Dawo da Kwamandan da Aka Dakatar Kan Zargin Karkatar da Tallafin Korona
Hisbah Ta Kano Ta Dawo da Kwamandan da Aka Dakatar Kan Zargin Karkatar da Tallafin Korona. Hoto: @daily_trust
Asali: Facebook

KU KARANTA: Abun Al’ajabi: Wata Mata Da Bata San Tana Ɗauke Da Juna Biyu Ba Ta Haihu a Jirgin Sama

"An umurce ni cewa in sanar da ku Babban Kwamandan Hisbah ya amince da mayar da Suyudi Muhammad Hassan a matsayin Kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Dala," a cewar wasikar.

An dakatar da kwamandan ne bayan Hukumar ta samu wasikar koke da ke zargin cewa ya karkatar da tallafin COVID-19.

An kafa kwamitin bincike domin tantance zargin da ake masa.

An dakatar da shi daga muƙaminsa duk da cewa an bar shi a matsayin ma'aikatu kafin a kammala binciken.

KU KARANTA: Kyauta Daga Allah: Wata Mata Ta Haifi Ƴan Tara a Morocco

Kwamitin ta gano cewa bai aikata dukkan abubuwan da ake zarginsa da aikatawa ba kawai an yi hakan ne don masa sharri.

Bayan dawowarsa, zai cigaba da aiki a matsayin Kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Dala.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel