Jerin jihohin da suka shirya biyan albashin naira 30,000

Jerin jihohin da suka shirya biyan albashin naira 30,000

Wasu gwamnoni a fadin kasar nan guda 9 sun bayyana cewa a shriye suke tsaf, domin amsa kiran shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan dokar da ya saka ta karin albashi zuwa naira 30,000, gwamnonin sunce babban burinsu shine su ga ma'aikatansu suna walwala

Gwamnatin jihar Kano, Zamfara, Kwara, Rivers, Kogi da kuma jihar Edo sun amince da tsarin karin albashi, sannan kuma sun yadda za su biya naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihohin.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce babban burin gwamnatinsa, shi ne ta ga ma'aikatan jihar suna walwala, kuma dalilin da yasa ba wani ma'aikaci da yake bin gwamnati kudi a jihar.

"A shirye muke mu biya naira 30,000 din, saboda jin dadin ma'aikatan mu shine burin gwamnatin mu," in ji Ganduje.

Jerin jihohin da suka shirya biyan albashin naira 30,000
Jerin jihohin da suka shirya biyan albashin naira 30,000
Asali: Twitter

Gwamnan Abdul'aziz Yari na jihar Zamfara ya ce, gwamnatinsa za ta yi iya bakin kokarinta domin tabbatar da jin dadin ma'aikatan jihar.

Yari wanda ya yi magana ta bakin mai bashi shawara ta musamman a fannin sadarwa, Malam Ibrahim Dosara ya ce, duk wata jiha da ta ke da tausayin ma'aikatan ta dole ta yi maraba da karin albashin ma'aikatan da gwamnatin tarayya ta yi.

Hakazalika ita ma gwamnatin jihar Osun ta ce za ta jira taga tsare-tsaren da za abi don fara biyan ma'aikatan naira 30,000 din.

Sakataren gwamnan jihar, Mista Adesina Adeniyi, shi ne ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi a wayar salula, ya ce tunda an riga an mayar da karin albashin dokar kasa, gwamnatin jihar kawai ta na jira a fitar da tsare-tsaren yadda biyan zai kasance.

Haka ita ma gwamnatin jihar Kwara ta gama shiryawa tsaf domin fara biyan ma'aikatan nata albashin, a cewar mai bawa gwamnan jihar Abdulfatah Ahmed shawara ta musamman fannin sadarwa, Dr. Muyideen Akorede.

Akorede ya ce ya tina lokacin da gwamnatin jihar ta tsara wata kwamiti wacce shugaban ma'aikata na jihar Modupe Susan ya jagoranta akan yadda za a tsara biyan albashi kowane wata, kafin shugaban kasar ya sanya hannu akan dokar karin albashin.

KU KARANTA: Ya datse hannunshi, saboda ya yi kuskure wurin kada kuri'a

Hakazalika gwamnatin jihar Kogi ta ce tunda har gwamnatin tarayya ta mayar da karin albashin doka to a shirye ta ke ta biya albashin.

Haka ita ma gwamnatin jihar Neja ta ce baza a barta a baya ba. Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce a shirye ya ke ya fara biyan ma'aikatan jihar albashin da gwamnatin tarayyar ta tsara.

Ita ma gwamnatin jihar Delta ta ce ta na jira gwamnatin tarayya ne kawai ta fitar da tsare-tsare yadda za a biya ma'aikatan don fara aiki dashi.

Gwamnan jihar Rivers Nyesom WIke, ya ce ya na lale da karin albashin da gwamnatin tarayyar ta yi kuma a shirye ya ke ya fara biyan ma'aikatan jihar tasa.

Gwamnatin jihar Edo ita ma ta ce baza a barta a baya ba wurin biyan albashin, domin kuwa za ta biya kowanne ma'aikaci hakkinsa, domin ganin walwala da jin dadin ma'aikatan jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel